An halaka shanu dubu talatin, kauyuka dari da tamanin, a rikicin Taraba

BY YERWA EXPRESS NEWS | JUNE 22, 2017

Fulani makiyaya da dama ne suka mutu a yayin wani hari da wasu masu daukan makamai suka kaddamar a Mambila, Karamar Hukumar Sardauna, Jihar Taraba.

Kazalika masu dauke da makaman sun halaka shanu da dama da sunan ramuwa.

Wakilin mu a Jalingo ya kawo rahoton cewa a kalla maharan, kodai sun kashe ko sace shanu dubu talatin, sannan kimanin kauyuka tamanin ne aka kona kurmus a yayin gudanar wannan rikici.

Shaidan gani-da-ido, da ya tsero daga karamar hukumar da ke fama da wannan rikici, ya shaidawa Jaridar YERWA EXPRESS NEWS a Jalingo cewa, masu dauke da makaman sun halaka kadarori da dama mallakin Fulani makiyayan.

'Tsakanin Litinin zuwa yau, an shafe daukacin iyalai hamsin, inji wani mai shaidar gani da idon'.

Kungiyar Fulani makiyaya ta Najeriya, mai suna Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria a turance, ta bayyana jimaminta a cikin wani sako da ta saki, inda ta bayyana wannan aiki a matsayin 'halaka maras kan gado'.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabannin al'ummar wannan yanki, ta koka kan harin da aka kai a kan kauyukan Fulani kusan dari da tamanin, a tsanin Mambila. Sun yi kiran gaggawa ga gwamnati da ta kawo 'daukí don gujewa shiga yanayi mai mummunar illa.

Ko da yake babu takamammen silar wannan rikici, hukumar 'yan Sanda na jihar Taraba ta dangana shi zuwa ga rashin jituwa tsakanin jam'iyyu biyu, wadanda tuni suke gaban kotu a Gembu.

'Kotun ta zantarwa wani mutum daga kabilar Mambila kaso a gidan yari, hukuncin da ya tunzura yaran wannan mutumi zuwa gidan wanda ya sa karan, wani bafulatani mai suna Mallam Riwi Ahmadu, tare da bukatar a saki mahaifinsu, kuma sukayi barazanar yin maganinsa'

Rikicin dai ya sha faruwa tun kafin wannan. A cewar 'yan sanda, 'rashin amsa bukatar sako wancan da aka tsare, shi ya sa yaran suka tabbatar da barazanar su ta hanyar cinna wuta a gidan mai karan, da samar da rauni a kanshi da kuma halaka kadarorin miliyoyin naira.

Mista David Misal na rundunar 'yan sanda, wanda yayi magana a madadin shugaban na 'yan sanda, ya bada rahoton kisan mutane bakwai, sannan ya shaida cewa an kawo halin da ake cikin bisa karkashin iko na hukuma, tare da kama wasu, an kuma tura ma'aikata, ciki har da kwamishinan 'yan sanda, Yakubu Buba, wanda tuni ya kaura zuwa yankin da abin ke faruwa.


Related: