''Mun samu dabinon Saudi'' - inji wasu 'yan gudun hijrah a Borno

BY YERWA EXPRESS NEWS | JUNE 21, 2017, 02:33 PM

A makon da ya wuce, anyi ta tabka muhara a shafukan sada zumunta kan wani al-amari mai tsarkakiya-wato bacewar dabino kimanin tan 200 da gwamnatin Saudi Arabiya ta bawa 'yan gudun hijra a Nijeriya.

Gidajen Yada labaru da dama sunyi rahotanni akai, inda suka bayyana cewa lamarin ya ta'azara. 

Kawo i zuwa yanzu, Jama'a masu fada a ji, na ta kokarin bankado inda ainihin dabinon suke.

Rahotanni na cewa, ana zargin  Hukumar dake lura da 'Yan gudun Hijra wadda alhakin raba dabino ke kanta, na da hannun aikata wannan badakalar. 

A ranar Asabar, 9 ga watan Yuni, 2017, hukumar dake lura da 'yan gudun hijra, ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana rawar da taka wajen sauke nauyi da ya rataya akanta, tare da yin ikirarin cewa an raba dabinon ga 'yan gudun dake yankin arewa maso gabas, Birnin Tarrayya Abuja da kuma wasu massallatai.

Tun kafin wannan sanarwa, karamar ministar harkokin waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, ta nemi afuwar gwamnatin Saudi Arabiya bisa faruwar wannan al-amari inda ta nuna takaicinta.

Jaridar Yerwa Express News, ta ziyarci wasu daga cikin sansanonin 'yan gudun hijra a yankin arewa maso gabas domin gano gaskiyar al-amarin, inda ta gano cewa;duk da cewa mafi yawan 'yan gudun hijran basuda masaniya kan kyautar dabino daga gwamnatin Saudi Arabiya amma abin mamaki, wasu sun samu.

Mal Abdulrahmna Habib, shugaban 'yan gudun hijra na karamar hukumar Damboa, dake Sansanin  bayan gari wato bye pass ya bayyana cewa " sun samu labarin dabinon ta radiyo, amma har yanzu bai iso garemu ba".

Mal Sherrif Kukawa, shugaban ,yan gudun hijra na karamar hukumar Kukawa, ya kara da cewa " ni da jama'ata  ba muda labarin dabino kuma bamuga komi ba".

Sai de, wakilinmu daga Jihar Gombe, inda gwamnati ta rufe duk sansanonin .yan gudun hijrah, ya shaida mana cewa mafi yawan 'yan gudun hijrah da ya hadu dasu a yayin wannan rahoto sun shaida masa cewa ko kwallon dabino basu gani ba balle dabino, sabanin abinda hukumar ke ikirari.

Lawan Mohammed, dan gudun hijrah ne, mazaunin Hammadu Kafi, ya kuma shaidawa wakilinmu cewa " in ba yanzu ba, ban samu labarin dabino ba".

Sai de kuma, 'yan gudun hijrah dake zaman mafaka a kwalejin Shari'a da addinin Islama na Mohammed Goni sunyi ikirarin samun dabinon.

Mallam Mohammed Abadam, dan gudun hijrah daga karamar hukumar Abadam, yace " ina zaune, aka bani dabino, kuma daga bisani na samu labarin wasu ma sun samu".

Mallam Ali ya kara da cewa, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA, ita ce ta raba musu dabino.

Dukkan yunkurin tuntubar hukumomin bada agajin gaggawa na jiha da na tarrayya domin jin ta bakinsu ya citura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Sauran bayanai na nantafe...


Related: