Solomon Dalung yayi amai ya lashe

Daga MUHAMMAD M ARI | YERWA EXPRESS NEWS, JUNE 07, 2017, 07:26 PM

A makon da ya gabata ne, Ministan wasanni kuma mabiyin addinin kirista, Barista Solomon Dalung, ya kai ziyarar sada zumunci wajen tafsirin babban malamin Izalah kuma shugaban Hukumar Raya Fasahar Bayanai Ta Kasa wato NITDA, Dr. Isa Ali Fantami, wanda yake gudanar wa a Masallacin An nuur dake babban birnin tarayya, Abuja.

Ziyarar da Ministan ya kai, ya bar baya da koora, saboda jim kadan bayan tafiyar sa daga taron, jita-jita su ka fara yaduwa cewa Ministan ya karbi addinin musulunci.

Hakan ya tunzura shi matuka, har yakai ga yin rubutu a shafinsa na sada zumunta wato facebook, mai taken "Gayyatar da Sheikh Fantami ya min zuwa musulunci rashin kyautatawa ce gare ni", inda a cikin wannan rubutun Ministan ya kira jama'ah da suyi watsi da jita-jitar cewa ya musulunta saanan ya kuma kara da cewa kamata yayi Sheikh Fantami ya same shi a gida ko ofis idan har da gaske yake son ya tallata masa shiga musulunci, ba kawai yayi amfani da ziyarar da yakai masa don karfafa zaman takewa da nufin kawo zaman lafiya mai dorewa don cin zarafinsa ba.

Wannan rubutu da Ministan yayi ya sake kawo cece-kuce tsakanin 'yan gwagwarmaya da dama a fadin kasar.

Abin mamaki, ministan de ya lashe aman da yayi a baya ta hanyar sake wallafa sabon rubutu a shafinsa na facebook mai taken 'neman yafiya zuwa ga dan uwa, aboki kuma Shugaba, Isah Pantami'.

A cikin wannan rubutu nasa ya nuna gazawarsa ta' dan Adam ce ta saka shi yin kakkausar magana a baya, don haka yana neman yafiya da jaddada kira ga Sheikh Fantami akan su cigaba da gwagwarmaya kamar yadda suka saba domin halayyarsu da sauran abubuwa nasu suna kama da juna.


Related: