Yaro mai kimanin shekaru 10 ya cinna wuta a gidan attajirai uku

BY MUHAMMAD M ARI, GOMBE | YERWA EXPRESS NEWS, JUNE 15, 2017, 10:34 PM

A daren jiya laraba ne, a cikin garin Bajoga, Karamar Hukumar Funakaye, ana zargin, wani yaro mai suna Osama, ya cinna wuta a gidajen wasu attajirai wadanda suka hada da; Alhaji Bappah Jurara, Alhaji Audi Maishinkafa da Alhaji Dahiru Direba.

Shi wannan yaro da ake zargi, 'dan asalin garin Bularafa ne, dake Jahar Yobe, ya zo garin Bajoga tare da mahaifansa kimanin shekara biyu kenan, a sanadiyyar gudun hijira da sukayi yayinda rikicin Bokoharam yayi kamari.

Tuni dai mazauna yankin suka mika yaron ga babban offishin Hukumar Jami'an tsaro na 'yan sanda na Bajoga. Sufeton 'yan sanda mai suna Kram, ya shaida wa wakilin Jaridar Yerwa Express cewa, 'wannan ba shine farau ba, domin kuwa a baya har ta kai ga korar yaron da mahaifansa daga garin na Bajoga dalilin irin wadannan katobara ta sa'.

Wakilin YERWA EXPRESS NEWS (YEN) ya samu damar tattanawa da wannan yaro da ake tuhuma Osama kuma ya shaida masa cewa 'shi kansa bai san lokacin da zuciyarsa ke sashi aikata irin wannan mummunan aiki Ba, duk da cewa shi ba mahaukaci bane. Osama ya kara da cewa shi baya yawo da ashana ko man fetur don cinna wutar'.

Babban Jami'in 'yan sanda na Bajoga, DPO Akin, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ya shaida mana cewa wannan shine karo na uku da ake tuhumar Osama da wannan laifi. Ya bayyana cewa, A karo na biyu ne suka iza keyarsa zuwa gidan kaso na yara wato Remand Home a turance dake Gombe, inda can ma Osama ake zargin ya tattara katifun gidan yarin ya kona.

DPO mai suna Akin ya ce a halin yanxu, suna shirin mika shi gidan kaso na yara kafin zuwa gaban kotu don ya fiskanci hukunci.

Sauran labaru za su biyo baya nan ba da jimawa ba...


Related: